No 1 Arewa's Platform

CONTACT US FOR MUSIC/VIDEO PROMOTION WHATSAPP: 07035500159/08033303306, gatanarewa09@gmail.com

ADS

Thursday, September 5, 2019

RIKICIN AFRICA TA KUDU
NEWS# WEF: Oby Ezekwesili da Jim Ovia sun halarci taron da ake yi a Afrika ta Kudu

Tsohuwar Ministar Najeriya, Misis Oby Ezekwesili, da shugaban bankin Zenith, Jim Ovia, sun jawo abin magana bayan da su ka halarci taron tattalin arzikin da ake yi a kasar Afrika ta Kudu.

Wadannan manyan mutane sun halarci taron ne a daidai lokacin da kasashen Afrika su ke kwayewa Afrika ta Kudu baya a dalilin harin da mutanenta su ka kai wa 'Yan Najeriya da wasu.

Rikicin da ake yi ya sa gwamnatocin kasashe har da Najeriya su ka janye daga wannan taro na WEF da aka shirya a Kudancin Afrikan. Duk da wannan Ezekwisili da Ovia ba su fasa halarta ba.

Oby Ezekwisili da Mista Jim Ovia su na cikin wadanda su ka jagoranci wani zama da aka yi wajen wannan taro na Duniya jiya. A da, an shirya cewa shugabannin Najeriya za su halarci zaman..

Rubuta MBW don samun labaran Hausa, wasu Karin labaran na jiranku.

No comments:

Post a Comment